Écoutez le conte : Wata rana sahara zata sake zama kore kamar da
Publié le :
Écouter - 03:17
Ku ji busawar iska, Sahara ce ke kuka. Ta na so ta dawo da kamaninta.
Ku ji busawar iska, Sahara ce ke kuka. Ta na so ta dawo da kamaninta.
Sahara dama asalinta ba Hamada ba ce. Da ita kasa ce kore mai kyau kuma. Mazaunan wurin suna darajanta halitta. Suna zama a wurin a cikin farin ciki. Suna kiwon tumaki, suna noma, suna kuma farauta. Suna kaunar kasarsu, kasar kuma na kaunar su.
Bayan haka sai ga makwadaita sun zo, sai bala’i ya yadu.
Ba neman kyautatawa al’umma suke soba, sai dai neman arzikin kasa. Kasar bata isarsu sai dai neman kari.farautar da sukeyi ba na ci bane, amma na nuna mazantaka.
Sun sare itatuwa, ba domin kare kansu ba, amma domin gina manya gidaje.
Wadannan marasa lumana sun ji ma sahara rauni mai tsanani har ta zama Hamada.
Duk da haka al’ummarta sun zauna a wurin domin suna kaunan ta. Wannan ya taba zuciyar Sahara. Domin ta nuna godiyan ta, sai ta basu tafki da kuma Gaban ruwan Niger.
Duk da haka, bata ji dadi ba.
Ku saurari busawar iska, Sahara ce ke kuka.tana so ta dawo da kamanninta .
Wata rana sai ga wani mai hikima ya zo. Sahara ta tambaye shi: Yaya zan iya mayar da zaman lumana irin ta da? Ka yi zumunci da masu adalci da kuma masu kirki, wadanda ke mutunta halitta. Ya kara da cewa wata rana wani mutum zai zo, zai sake rayar da ciyayi da kuma itatuwa da ke tsira a da. Wannan mutum mai adalci , zai sadakar da ransa domin itatawan ku.
Amma kamin ya dawo da aljannar da ta bace , dole ne ya kori makwadaita. Wannan ba zai zama aiki mai sauki ba. Amma Allah ya sa, akwai mai adalci wanda zai taimaka masa, ya yi nasara bisan matsalolin, da kuma abokan gabansa.
Wannan mutumin na dauke da iri wanda zai sa Sahara ta dawo kamar da.
Ku ji busawar iska, Sahara ce ke kuka. Ta na so ta dawo da kamaninta.
Tana jiran wani mai adalci wanda zai maida ita kore kamar da.
Yayin da ka ke darajanta halitta, haka nan za ka dinga kaunarta, haka kuma zaka hanzarta rayar da ita.